Emenalo ya ajiye aikin darakta a Chelsea

Asalin hoton, Chelsea FC
Emenalo tsohon dan wasan Enugu Rangers ya koma Chelsea a 2007
Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Nigeria, Michael Emenalo ya ajiye aikin daraktan tsare-tsare a kungiyar Chelsea.
Emenalo wanda ya buga wa Super Eagles wasa 14, ya koma Chelsea a 2007 a matsayin mai farauto 'yan kwallo a lokacin Avram Grant, bayan da Ray Wilkins ya bar kungiyar.
A watan Nuwambar 2010 kungiyar ta nada shi mataimakin koci daga baya ta ba shi mukamin daraktan tsare-tsere, inda aikin shi ya hada da tsara yadda matasan Chelsea za su samu kwazo domin buga wa babbar kungiyar.
A tsawon lokacin da Emenalo ya yi aiki a Stamford Bridge, Chelsea ta lashe kofin Premier uku da FA uku da League Cup da kofin Zakarun Turai na Europa da na Champions League.