Pirlo ya yi ritaya daga buga tamaula

Pirlo

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Pirlo ya ci kofin duniya a 2006 tare da tawagar kwallon kafar Italiya

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Italiya, Andrea Pirlo ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa, bayan da ya yi wasa na karshe a New York City.

Dan kwallon mai shekara 38, ya buga wa Italiya wasa 116 ya kuma lashe kofin duniya a tawagar a shekarar 2006.

Pirlo ya fara murza-leda a matshin dan kwallo a Brescia daga nan ya koma Inter Milan da AC Milan da kuma Juventus, daga baya ya koma buga gasar Amurka shekara biyu da ta wuce.

Dan wasan wanda ya yi shekara 22 yana taka-leda ya ci kofin Serie A biyu a Milan da kofin Zakarun Turai na Champions League da kofin duniya na Zakarun nahiyoyi a 2003 da kuma 2011.

Pirlo yana daga cikin 'yan wasan da suka ci kofin Serie A hudu a Juventus tsakanin 2012 zuwa 2015.