'Yan Madrid 13 aka gayyata tawagar kasashensu

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

Bayanan hoto,

'Yan wasan Real Madrid 13 ne za su buga wa kasashensu wasanni zuwa karshen mako

Kimanin 'yan wasan Real Madrid 13 ne aka gayyata tawagar kwallon kafar kasashensu domin buga musu tamaula.

Daga cikin 'yan wasan Sergio Ramos da Nacho da Isco da Asensio da Varane da Kroos da Casemiro da kuma Marcelo, za su buga wa kasashen su wasan sada zumunta.

Su kuwa Modric da kuma Achraf za su buga wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin dunuya da za a yi a Rasha a 2018.

Sauran 'yan wasa da suka hada da Vallejo da Ceballos da kuma Mayoral za su fafata ne a wasan shiga gasar cin kofin matasa 'yan 21 ta Turai da za a yi a 2019.

Real Madrid tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 27, za kuma ta ziyarci Atletico Madrid a wasan mako na 12 a gasar La Liga a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba.