Ronaldo zai dawo kan ganiyarsa a La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ronaldo ya ci kwallo shida a gasar cin kofin Zakarun Turai, inda Harry Kane keda biyar a raga

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo, na fatan zai dawo kan ganiyarsa a fagen cin kwallaye a gasar La Liga ta Spaniya a bana, bayan da aka buga wasannin mako na 11.

A labarin da jaridar marca ta wallaha ta ce dan kwallon bai damu da kanfar cin kwallaye da yake fama a gasar ta La Liga ba.

Ronaldo ya ci kwallo daya ne kacal a gasar ta bana, a karawar da Real Madrid ta ci Getafe 2-1 a ranar 14 ga watan Oktoba.

Sai dai kuma dan kwallon bai buga wasan La Liga hudu ba, sakamakon dakatar da shi wasa biyar da aka yi a lokacin Super Cup na Spaniya da suka kara da Barcelona.

Wasannin hudun da bai buga ba sun hada da karawa da Deportivo La da Valencia da Levante da kuma Real Sociedad.

Sai dai kuma dan kwallon na tawagar Portugal shi ne na daya a yawan cin kwallo a Gasar cin Kofin Zakarun Turai, inda ya ci shida.