Gwarzon dan kwallon BBC na 2017: Wane ne Naby Keita?

Keita Naby Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Naby Keita madugu ne a kasarsa ta Guinea

Watakila Naby Keita ya kasance dan kwallon da ba a san shi ba a Jamus a kakar wasanni ta 2016-17, to amma kuma sai ga shi sunansa ya fado cikin jerin shahararrun 'yan wasa 11 da aka zaba a kungiyar Bundesliga na shekara.

Dan wasan na Guinea ya samu kuri'un jama'a fiye da duk wani dan wasan tsakiya da ke taka leda a Jamus.

Kungiyar Red Bull Leipzig na daya daga cikin wadanda suka yi bazata a kakar wasanni ta 2016-17 kasancewar kulob din na biyu a teburin gasar Bundesliga sannan kuma ta samu damar yin katabus a gasar zakarun Turai ta Champions League sakamakon kwazon Keita.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
kalli bayani game da Naby Keita

Minti biyar da fara wasansa na farko a gasar ta Bundesliga, Keita wanda aka saya daga kulob din kasar Austria wato Red Bull Salzburg ya ci wa Red Bull Leipzig kwallo a wasansu da Borussia Dortmund abun da ya bude ma sa kofar zama gwarzon shekara a kungiyarsa da Bundesliga.

Keita ya jefa jimullar kwallaye 8 a gasar Bundesliga, inda kuma ya taimaka aka ci kwallaye guda bakwai. Wani abu da ya kara wa dan wasan mai shekaru 22 kima shi ne kasancewar sa dan baya mai kyau.

Saboda a duk wasa irin kwallon da Keita yake bugawa ce ke kayatar da 'yan kallo.

Kasancewar Keita dan wasan tsakiya da ke shafa leda gaba da baya, kuma ba ya wasa da zarar ya sami kwallo wanda hakan ke firgita abokan gaba har suke bayyana shi kamar daya tamkar dan wasa biyu, al'amarin da ya janyo masu horar da 'yan wasa ke kaunar sa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Naby Keita yana taka rawar gani a kulob din Red Bull Leipzig na Jamus

Keita kwararre ne a sarrafa kwallo, yana da kuzari da basirar hangen nesa wajen yi wa abokan wasa tazara (Alkalumma sun nuna ya fi dan wasan Bayern Munich Arjen Robben yawan yanke a kakar da ta gabata), yakan ci kwallo ya kuma mika a ci.

Wani abun mamaki shi ne yadda kocinsa a Leipzig wato Ralph Hasenhuttl ya danganta shi a matsayin dan wasa mafi muhimmaci, wanda basirarsa ta taka leda ba a saba ganin irinta ba.

Keita wanda aka Haifa a birnin Conakry ya janyo hankalin kungiyar Liverpool har ta sanya makudan kudi da ba ta taba zuba wa ba domin sayen wani dan wasan Afirka, inda ta sanya £48m kan dan wasan domin taka mata leda a 2018. Sai dai kuma daga baya kungiyarsa ta Leipzig ta yi da-na-sanin sayar da shi.

Sunan Keita na daga jerin sunayen 'yan wasan da ke fatar buga wa Guinea wasa a Russia a 2018 kuma koda dan wasan ya ci wa kasarsa kwallaye a wasannin neman cancantar shiga gasar da ta fafata da Libya da Tunisia, to za a iya cewa Guinea ba ta samu cancantar ba cikin sauki.

Keita ya ce a har kullum Yaya Toure ne gwaninsa. Saboda haka yanzu abin tambaya shi ne ko Keitan zai iya yin irin abin da Toure ya yi ta hanyar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka a jerin kyaututtukan da ya lashe?