Kun san Sadio Mane?

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sadio Mane da wasa ne mai zafin nama

Sadio Mane Dan wasan Senegal da Liverpool kakarsa sa yi kyau a 2017, Kuma kamar yadda aka zabi dan wasan cikin jerin tawagar zaratan 'yan wasan PFA na bana a ingilia, yana kuma cikin 'yan wasan Afrika biyu a cikin jerin sunayen 'yan wasan da aka zabo domin lashe kyautar Ballon d'Or.

Ya kuma taka rawar gani wajen taimakawa Senegal shiga gasar cin kofin duniya a karo na biyu, nasarar da ba su samu ba tun shekarar 2002.

A bana Mane ya ci wa Senegal kwallaye hudu.

A farkon shekara, Mane ya dace da irin rawar da ya ke takawa, ya iya zarra, ga yanke da karfin iya cin kwallaye a raga.

Ko da yake Mane ya fuskanci kalubale a shekararsa ta bana, domin duk da ya ci wa Senagal kwallaye biyu a wasannin rukuni a gasar cin kofin Afrika, amma ya barar da fanareti a wasan dab da na kusa da na karshe, wannan ne kuma ya karfafawa kamaru guiwar zuwa ta lashe kofin gasar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ko kun san waye Sadio Mane?

A lokacin Mane, da idon duniya ya koma a kansa ya shatata kuka, domin ya barar da damar shiga sahun zaratan 'yan wasa da suka taba lashe kofin Afrika.

Sai dai kuma hakan ya yi wa Liverpool da magoya bayanta dadi domin nasara daya ne kacal kungiyar ta samu a wasanni 7 da ta buga bayan tafiyar Mane wakiltar kasarsa a gasar cin kofin Afrika.

Da dawowarsa ne Mane ya taimakawa Liverpool samun galaba akan Tottenham da ci 2-0, daga bisani kuma ya ci wa Liverpool muhimman kwallaye a nasarar da ta samu akan abokan gaba Arsenal da Everton.

Hakkin mallakar hoto Stu Forster
Image caption Sadio Mane yana cikin 'yan wasan da Liverpool take ji da shi

Mane ya nuna yana da matukar muhimmaci a Liverpool.

An kammala Kakar da ta gabata Mane na da kwallaye 13 a premier, duk da ya shafe wata biyu yana jinyar tiyata da aka yi ma sa a guiwarsa tsakanin Afrilu zuwa Mayu.

Kuma duk da haka Mane a kakarsa ta farko a Liverpool ya yi kafada da Coutinho, da yawan kwallaye a kungiyar duk kuwa da ya kauracewa wasanni da dama.

Mane ya taimakawa Liverpool shiga gasar zakarun Turai a karon farko bayan shekaru takwas.

Dan wasan na Senegal ne Liverpool ta ba kyautar gwarzon shekara.

An auna cewa Liverpool ta fi samun nasara idan Mane yana fili, sabanin idan babu shi.

To la'akari da muhimmacinsa a Liverpool, dan wasan na Senegal mai shekaru 25 na fatar lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na BBC a karon farko bayan shekaru uku yana nema.