Super Eagles za ta kara da Algeria

Super Eagles

Asalin hoton, The NFF

Bayanan hoto,

Super Eagles ba ta je gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Gabon a bana ba

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta ziyarci Algeria domin buga wasan karshe na rukuni na biyu a fafatawar zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Nigeria wacce ita ce kasar farko a Afirka da ta samu gurbin zuwa Rasha a gasar da za yi a badi, za ta kece raini da Algeria a ranar Juma'a a Constantine.

Super Eagles ta jagoranci rukuni na biyu ne da maki 13 a wasa biyar da ta buga, ita kuwa Algeria tana ta hudu ta karshe da maki daya kacal.

Zambia ce ta biyu a rukunin da maki bakwai, sai Kamaru ke biye da maki shida, a kuma ranar Asabar ce Zambia za ta karbi bakuncin Kamaru.