Super Eagles ta hada maki 14 a wasa shida

Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Super Eagles ce ta fara samun tikitin kai wa Rasha a nahiyar Afirka

Tawagar kwallon kafar Nigeria ta Super Eagles ta hada maki 14 a karawa shida da ta buga a wasannin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Super Eagles wacce ita ce ta farko da ta samu tikitin zuwa buga gasar kofin duniya daga Afirka ta tashi wasa 1-1 da Algeria a ranar Asabar.

Hakan ne ya sa Nigeria take ta daya a rukuni na biyu a wasannin shiga gasar cin kofin duniya a wasa shida da ta yi jumulla, ta ci karawa hudu ta yi canjaras biyu ta kuma ci kwallo 12 an zura mata 4 a raga.

Zambia wacce take ta biyu a runin na biyun da maki bakwai za ta karbi bakuncin Kamaru mai maki shida kuma ta uku a teburin da za su kara a ranar Asabar.

Ga sakamakon wasannin da Super Eagles ta buga:

  • Zambia 1-2 Nigeria
  • Nigeria 3-1 Algeria
  • Nigeria 4-0 Kamaru
  • Kamaru 1-1 Nigeria
  • Nigeria 1-1 Zambia
  • Algeria 1-1 Nigeria