Gwarzon dan kwallon Africa na BBC: yau ce ranar karshe

Aforty2017
Image caption 'Yan wasa biyar da za a zabi gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017

An bayyana 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC na 2017 su biyar da suka hada da Pierre-Emerick Aubameyang da Naby Keita da Sadio Mane da Victor Moses da kuma Mohamed Salah, an kuma bude kada kuri'a domin zabo wanda zai lashe kyautar bana.

Domin yin zabe latsa nan

Ga tarihin 'yan wasan da gwawarmayar da suka yi da sashen wasanni na BBC ya shirya:

PIERRE-EMERICK AUBAMEYANG -Dan wasan Gabon da Borussia Dortmund

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan ne karo na biyar a jere da Aubameyang ke cikin 'yan takara

Ba a taba samun wani dan Afirka ba wanda ya fi kowa cin kwallaye a gasar Bundesliga har sai da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallaye 31 a kasar wasan 2016-17.

Wannan nasara ba wai kawai ta bai wa dan wasan dan asalin kasar Gabon damar dusashe tauraruwar dan wasan kasar Ghana, Tony Yeboah ba, wanda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye har karo biyu a 1990, Pierre ne mutum na hudu a duniya da ya zarga kwallaye 30 a raga a gasar Bundesliga, irinsa na farko a tsawon shekara 40.

Wani kuma abun ban sha'awa dangane da nasarar fitaccen dan wasan na kungiyar Dortmund shi ne yadda ya ci kwallayen 31 a jerin wasanni 32, al'amarin da ya sanya kulob din nasa kasancewa na daya a gasar ta Bundesliga har karo biyu a jere sakamakon baiwar gudu da ta cin kwallaye da Allah ya huwace masa.

Kwallaye ukun da ya ci kulob din Benfica a wasa daya, a watan Maris ne suka sanya kididdigar jumullar kwallayen da dan wasan ya ci suka zama 40 a gasar Zakarun Turai ta Champions League. Kwallon da ya ci a wasan da kulob dinsa ya ci Eintracht Frankfurt 2-1 wadda ta bai wa Dortmund damar daukar kofi a gasar wasan kwallon kafar Jamus na daya daga cikin kwallayen da ya ci 40.

Sakamakon kwazon Aubameyang mai shekara 28 ne ya sa aka sanya sunansa a jerin sunayen 'yan wasan da za a zabi gwarzon dan wasan duniya na FIFA. kuma Aubameyang ne dan wasa daya tilo daga Afirka a jerin 'yan wasan na FIFA, ko da yake Sadio Mane da suke takara tare domin lashe kyautar gwarzon Afrika na BBC yana cikin jerin 'yan wasan da ke takarar lashe kyautar Ballon d'Or.

Duk da tsammanin da ake da shi cewa dan wasan dan kasar Gabon wanda dan gayu ne zai bar kulob din Dortmund a karshen kaka har yanzu hakan bai kasance ba. Manyan kungiyoyin wasa kamar Paris Saint-Germain da Manchester City sun nuna sha'awarsu kan dan wasan. Sai dai kuma dan wasan ya dade yana burin buga wa kulob din da kakansa ya fi so wato Real Madrid, wasa, amma har yanzu burinsa bai cika ba sakamakon rashin nuna sha'awarsa, duk kuwa da irin baiwar cin kwallaye da ya nuna a Dortmund tun 2013.

Bugu da kari, a yanzu haka kwallayen da Aubameyang ya ci 135 a wasanni 204 na nufin zai iya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a kulob din Dortmund, kuma hakan na nufin zai iya zarta Michael Zorc daga nan zuwa karshen shekara.

'Auba' kara kwazo yake yi fiye da abun da ya yi a baya, a inda ya zura kwallaye takwas a wasanni shidan farko na gasar Champions League.

To sai dai idan an diba batun kimar kasar dan wasan ta asali wato Gabon a kwallon duniya, za a iya cewa kyaftin Aubameyang bai ji dadin yadda kasar tasa ta kasa kai bantanta a gasar zakarun kwallon kafar nahiyar Afirka ba duk kuwa da cewa shi ne mutumin da ya jefa kwallaye biyu a wasanni uku. Abun tambaya a nan shi ne ko rawar da yake takawa a Dortmund za ta ba shi damar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka?

Naby Keita - Dan wasan Guinea da RB Leipzig

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Keita ya ci kwallo takwas a Bundesliga ya kuma taimaka aka ci bakwai, dalilin da ya sa shi ne fitatcen dan kwallon tsakiya a Jamus

Watakila Naby Keita ya kasance dan kwallon da ba a san shi ba a Jamus a kakar wasanni ta 2016-17, to amma kuma sai ga shi sunansa ya fado cikin jerin shahararrun 'yan wasa 11 da aka zaba a kungiyar Bundesliga na shekara. Dan wasan na Guinea ya samu kuri'un jama'a fiye da duk wani dan wasan tsakiya da ke taka leda a Jamus.

Kungiyar Red Bull Leipzig na daya daga cikin wadanda suka yi bazata a kakar wasanni ta 2016-17 kasancewar kulob din na biyu a teburin gasar Bundesliga sannan kuma ta samu damar yin katabus a gasar zakarun Turai ta Champions League sakamakon kwazon Keita.

Minti biyar da fara wasansa na farko a gasar ta Bundesliga, Keita wanda aka saya daga kulob din kasar Austria wato Red Bull Salzburg ya ci wa Red Bull Leipzig kwallo a wasansu da Borussia Dortmund abun da ya bude ma sa kofar zama gwarzon shekara a kungiyarsa da Bundesliga.

Keita ya jefa jimullar kwallaye 8 a gasar Bundesliga, inda kuma ya taimaka aka ci kwallaye guda bakwai. Wani abu da ya kara wa dan wasan mai shekaru 22 kima shi ne kasancewar sa dan baya mai kyau.

Saboda a duk wasa irin kwallon da Keita yake bugawa ce ke kayatar da 'yan kallo.

Kasancewar Keita dan wasan tsakiya da ke shafa leda gaba da baya, kuma ba ya wasa da zarar ya sami kwallo wanda hakan ke firgita abokan gaba har suke bayyana shi kamar daya tamkar dan wasa biyu, al'amarin da ya janyo masu horar da 'yan wasa ke kaunar sa.

Keita kwararre ne a sarrafa kwallo, yana da kuzari da basirar hangen nesa wajen yi wa abokan wasa tazara( Alkalumma sun nuna ya fi dan wasan Bayern Munich Arjen Robben yawan yanke a kakar da ta gabata) yakan ci kwallo ya kuma mika a ci.

Wani abun mamaki shi ne yadda kocinsa a Leipzig wato Ralph Hasenhuttl ya danganta shi a matsayin dan wasa mafi muhimmaci, wanda basirarsa ta taka leda ba a saba ganin irinta ba.

Keita wanda aka Haifa a birnin Conakry ya janyo hankalin kungiyar Liverpool har ta sanya makudan kudi da ba ta taba zuba wa ba domin sayen wani dan wasan Afirka, inda ta sanya £48m kan dan wasan domin taka mata leda a 2018. Sai dai kuma daga baya kungiyarsa ta Leipzig ta yi da-na-sanin sayar da shi.

Sunan Keita na daga jerin sunayen 'yan wasan da ke fatar buga wa Guinea wasa a Russia a 2018 kuma koda dan wasan ya ci wa kasarsa kwallaye a wasannin neman cancantar shiga gasar da ta fafata da Libya da Tunisia, to za a iya cewa Guinea ba ta samu cancantar ba cikin sauki.

Keita ya ce a har kullum Yaya Toure ne gwaninsa. Saboda haka yanzu abin tambaya shi ne ko Keitan zai iya yin irin abin da Toure ya yi ta hanyar lashe kyautar BBC ta dan kwallon Afirka a jerin kyaututtukan da ya lashe?

Sadio Mande - Dan wasan Senegal da Liverpool

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mane daya ne daga cikin 'yan wasan Afirka biyu da suke takarar kyautar Ballon d'Or

Sadio Mane Dan wasan Senegal da Liverpool kakarsa sa yi kyau a 2017, Kuma kamar yadda aka zabi dan wasan cikin jerin tawagar zaratan 'yan wasan PFA na bana a ingilia, yana kuma cikin 'yan wasan Afrika biyu a cikin jerin sunayen 'yan wasan da aka zabo domin lashe kyautar Ballon d'Or.

Ya kuma taka rawar gani wajen taimakawa Senegal shiga gasar cin kofin duniya a karo na biyu, nasarar da ba su samu ba tun shekarar 2002.

A bana Mane ya ci wa Senegal kwallaye 4.

A farkon shekara, Mane ya dace da irin rawar da ya ke takawa, ya iya zarra, ga yanke da karfin iya cin kwallaye a raga.

Ko da yake Mane ya fuskanci kalubale a shekararsa ta bana, domin duk da ya ci wa Senagal kwallaye biyu a wasannin rukuni a gasar cin kofin Afrika, amma ya barar da fanareti a wasan dab da na kusa da na karshe, wannan ne kuma ya karfafawa kamaru guiwar zuwa ta lashe kofin gasar.

A lokacin Mane, da idon duniya ya koma a kansa ya shatata kuka, domin ya barar da damar shiga sahun zaratan 'yan wasa da suka taba lashe kofin Afrika.

Sai dai kuma hakan ya yi wa Liverpool da magoya bayanta dadi domin nasara daya ne kacal kungiyar ta samu a wasanni 7 da ta buga bayan tafiyar Mane wakiltar kasarsa a gasar cin kofin Afrika.

Da dawowarsa ne Mane ya taimakawa Liverpool samun galaba akan Tottenham da ci 2-0, daga bisani kuma ya ci wa Liverpool muhimman kwallaye a nasarar da ta samu akan abokan gaba Arsenal da Everton.

Victor Moses - Dan wasan Nigeria da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Moses ya ci kofin Premier League a Chelsea bayan da ya nuna kwarewarsa a tamaula a Stamford Bridge

Lokacin da Victor Moses ya waiwayi tarihin wasansa, akwai yiwuwar dan wasan Najeriyan da kuma kungiyar Chelsea, ya ce kakar shekarar 2016 zuwa 2017 ce ta fi muhimmanci a gare shi.

Bayan shekarun da ya yi wasa a matsayin aro, daga bisani ne ya koma Chelsea - inda ya zama daya daga cikin manyan 'yan wasa da suka taka muhimmiyar rawa wajen lashe kofin firimiya.

A ranar 1 ga watan Oktoba ne kocin Chelsea, Antonio Conte ya gwada sanya Moses a wasan da suka doke Arsenal da Liverpool, inda kocin ya gwada salon 3-4-3.

Wannan ne wasansa na farko a Chelsea a cikin fiye da shekara uku, amma Moses ya rika nuna kwazonsa da basirarsa.

Wasan da suka doke Hull City yana cikin wasanni 13 a jere da Chelsea ba ta sha kayi ba, kuma na 22 da Moses ya buga, sai dai daga bisani ya shiga jinyar raunin da ya ji a watan Afrilu.

A watan da ya gabata ne dan wasan ya kara sanya hannu a wani sabon kwantiragi da kolub din Chelsea, inda zai ci gaba da taka leda kungiyar, wadda ya fara koma a shekarar 2017.

Conte ya bukaci sabunta kwantiraginsa ne saboda yadda ya kara ganin kwarewar Moses a wannin share fagen fara kaka.

Dan wasan mai shekara 26, ya ce yana samun nasara ta hanyar nuna kwazo da natsuwa da kuma zafin nama.

Bayan lashe gasar firimiya, Moses yana cikin 'yan wasan Chelsea da suka zo na biyu a gasar Kofin FA, bayan Arsenal ta doke su, inda Moses ya samu jan kati.

Moses ya buga wa kasarsa wasa ne sau uku kadai a bana, amma a wasansa na farko ya ci kwallo a karawar da Najeriya ta doke Kamaru da ci 4-0, abin da ya sa Najeriya ta samu damar zuwa gasar Cin Kofin Duniya.

Mohammad Salah - Dan wasan Masar da Liverpool

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Salah ne ya ci fenaritin raba gardama da ya kai Masar gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018, bayan rabon da ta je tun 1990

Abu daya zai sa ba za a taba mantawa ba da Mohammed Salah a tarihin kwallon kafa a Masar, saboda kwallo mafi muhimmaci da ya ci wa kasarsa a ragar Congo ana dab da a hure wasan da suka kara a watan Oktoba, wanda ya ba kasar nasarar shiga gasar cin kofin duniya karon farko bayan shekaru 27.

Sau bakwai Masar na lashe kofin Afrika amma tun1990 rabon da kasar ta je gasar cin kofin duniya. Salah ne ya taimakawa kasar tsallakewa bayan ya ci fanareti a wasan da suka tashi ci 1-1 da Congo. Cin kwallon ke da wuya murna ta barke da shagali a ciki da wajen filin wasan.

Duk da cewa Salah ya dade yana cin kwallaye, amma tarihi ba zai taba mantawa da shi ba a Masar, domin ya wadatar da 'yan kasar daga kishirwar da suka dade suna fama.

Salah ya samu yabo da girmamawa daga shugaban Masar Abdel Fatah al-Sisi.

Cin kwallon ne ya sa 'yan kasar ke yi wa Salah da kirari a matsayin "Sarkin Masar mai zamani" domin ko baya ga kwallon da ya ci a ragar Congo, Salah ya jefa kwallaye biyar a raga a wasannin bakwai da suka tsallakar da Masar zuwa Rasha.

Salah ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a 2017, inda ya shiga sahun 'yan wasa 11 da aka zabo mafi shahara a gasar, bayan ya ci kwallaye biyu tare da taimakawa aka ci hudu. Sannan ya taimakawa kasarsa zuwa matakin karshe a gasar, ko da yake Kamaru ce ta lashe kofin na Afrika.

Baya ga kasarsa, Salah sananne ne wajen cin kwallaye a kungiyoyin da ya ke taka leda musamman a Roma da Liverpool.

Tauraron Salah ya kara haskawa bayan ya dawo liverpool a watan Yuni, inda a watannin Agusta da Satumba aka bayyana shi a matsayin gwarzon dan wasan Liverpool.

Salah ya ci kwallaye 7 a wasannin Premier 11 da ya bugawa Liverpool, tare da cin kwallaye 5 a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai 6 da Liverpool ta buga.

A zamanin da yana Italiya, Salah ya taimaka wajen farfado da martabar Roma a Seria A, a kakar wasa daya da ya buga wa kungiyar inda ya ci kwallaye 15 tare d bayar wa aka ci kwallaye 11 a Lig . Kuma an kammala kakar 2016/2017 Roma na matsayi na 2 a teburin lig, tazarar maki hudu tsakaninta da Juventus.

Thierry Henry ya danganta Salah a matsayin dan wasa na musamman, amma ko dan wasan zai iya zama dan kasar Masar na farko da zai iya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na BBC bayan Mohamed Aboutrika da ya lashe kyautar a 2008.