Kasashe biyar daga Afirka da za su Rasha a 2018

World Cup Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasashe biyar ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci

An samu kasashe biyar da za su wakilci Afirka a gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Tun a ranar Juma'a Senegal ta samu tikitin zuwa Rasha, bayan da ta doke Afirka ta Kudu har gida da ci 2-0, hakan ya sa ta hada maki 11 a rukuni na hudu, Sai Afirka ta Kudu mai maki 6.

A ranar Asabar Morocco ta samu damar kai wa gasar da za a yi a Rasha bayan da ta ci Ivory Coast har gida 2-0, hakan ya sa ta hada maki 12 a rukuni na uku.

A dai ranar Asabar din Tunisia ita ma za ta wakilci Afirka a Rasha a badi, duk da tashi wasa da ta yi babu ci tsakaninta da Libya, wanda hakan ya sa ta samu maki 14, Jamhuriyar Congo ta kare da maki 13.

Tun farko Nigeria ce ta fara samun tikiti a Rasha, bayan da ta ja ragamar rukuni na biyu duk da saura wasa daya ya rage, inda ta hada maki 14, bayan da ta tashi 1-1 da Algeria a ranar Juma'a.

Ita ma Masar ta kai bantenta, bayan da ta yi ta daya a rukuni na biyar da maki 12. Kuma ita ce ta biyu a samun matakin zuwa Rasha daga Afirka.