Dan Aminu ya buge Balan Kwarkwada
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dan Aminu ya buge Balan Kwarkwada

Dambe 12 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Daga cikin wasannin har da wanda Dan Aminun Langa-Langa daga Arewa ya buge Balan Kwarkwada daga Kudu, kuma a karon farko da ya yi nasara tun bayan da suka dade suna dambatawa.

Mohammed Abdu Mamman Skeeper ne ya hada rahoton

Wasu wasannin da aka yi kisa sun hada da Garkuwan Mutanen Karmu daga Arewa da ya buge Shagon Mai Keffi daga Kudu a turtmi na biyu.

Shi kuwa Bahagon Dan Sama'ila daga Kudu ya doke Shagon Bahagon Soja a turmin farko.

Sauran wasannin canjaras aka yi:

  • Shagon Bahagon Soja daga Arewa da Shagon Dan Sama'ila
  • Shagon Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Shagon Dogon Auta daga Kudu
  • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Alaye daga Kudu
  • Usher daga Arewa da Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu
  • Shagon Shagon Dan Sama'ila daga Kudu da Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa
  • Nokia daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu
  • Sani Mai Kifi daga Arewa da Bahagon Aleka daga Kudu
  • Bahagon Aleka daga Kudu da Sani Mai Kifi daga Arewa
  • Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Bahagon Mai Maciji daga Kudu

Labarai masu alaka