Giggs zai yi darakta a makarantar kwallon Vietnam

Ryan Giggs Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ryan Giggs ya buga wa Manchester United wasa 963 ya kuma yi wa tawagar Wales fafatawa 64

Tsohon dan kwallon Manchester United, Ryan Giggs ya karbi aikin tuntuba a matsayin daraktan makarantar koyon tamaula ta Vietnam.

Giggs mai shekara 43, zai yi aiki a cibiyar tara kudi don zakulo matasan tamaula masu fasaha ta Vietname, domin horar da 'yan wasa da kuma koci-koci.

Tsohon dan wasan tawagar Wales, ya amince da yarjejeniyar shekara biyu, inda zai dinda zuwa Vietnam sau biyu a shekara domin gabatar da aikinsa.

Rabon da Giggs a dama da shi a fagen kwallon kafa tun bayan da Manchester United ta sallami Luis van Gaal a watan Mayun 2016.

A mako mai zuwa Giggs zai ziyarci Vietnam domin bikin kaddamar da shi, inda Paul Scholes ne zai zama babban bako a bikin.

Labarai masu alaka