Ta yaya Nigeria za ta tunkari Messi, Auguero da...?

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lionel Messi ya addabi Najeriya a wasan da suka kara a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014

Da yammacin ranar Talata ne tawagar kwallon kafa ta Najeriya za ta kara da takwararta ta Ajantina a wani wasan sa da zumunci na shirya wa gasar cin kofin duniya.

Shin Najeriya tana da karfin rike tawagar Ajantinan Messi kuwa?

A gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014, Lionel Messi ne ya ci Najeriya kwallaye biyu a kayen da ta sha a hannun Ajantina da ci 3-2 a zagaye na farkon gasar.

A wannan wasan ne kuma dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya zama dan wasan Najeriya na farko da ya fara cin kwallaye biyu a wasa daya cikin gasar cin kofin duniya.

Lionel Messi dai ya ci kwallaye sama da 600 wa kasarsa da kungoyin kwallon kafar da ya murza wa leda.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hare-haren da Messi ya kai wa Najeriya sun sa mai tsaron gidan Najeriya na wancan lokacin, Vincent Enyiama, ya tsokane shi.

Kuma a wasan Ajantina da Najeriya a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 Messi ya yi ta kai wa 'yan Super Egales hare-hare ta yadda mai tsaron gidan Najeriya na wancan lokacin Vincent Enyeama ya yi ta tsare kwallaye.

Sai dai kuma idan aka yi la'akari da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da Najeriya ta buga da kuma adadin kwallayen da aka sha ta, za a lura cewa masu tsaron bayan Najeriya suna da 'rowar kwallo.'

Najeriya ta buga wasanni shida kuma ta ci kwallaye 12 yayin da aka ci ta kwallaye 4, lamarin da ya sa ta kasance kasar da aka ci mafi karancin kwallaye a cikin jerin kasashen da suka nemi shiga gasar cin kofin duniya daga Afirka a teburin rukunin B.

Yaya Najeriya za ta yi da Ajantina idan babu Messi?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sai da kuma Vincent Enyeama da ya yi ta kare Najeriya daga hare-haren Messi ya dade bai buga wa Najeriya wasa ba.

Wasu rahotanni sun ce Lionel Messi ba zai buga wasan sada zumunci tsakanin kasarsa da Najeriya ba. Shin wannan na nufin babu wata matsala kenan ga Najeriya?

Tarihin wasannin Najeriya da Ajantina ya nuna cewa ko a lokutan da babu Messi ma Najeriya tana shan wahala a hannun Ajantina.

A gasar cin kofin duniya ta shekarar 1994 inda Najeriya ta fara haduwa da Ajantina tawagar Super Eagles ta Najeriya ta sha kaye a hannun Ajentina da 2-1 inda Claudio Cannigia ya ci Najeriya kwallaye biyu kuma Samson Siasia ya ci Ajantina kwallo daya.

Da kasashen suka sake haduwa a shekarar 1995 a gasar zakarun nahiyoyi, sun yi canjaras ne babu ci ko daya.

Amman a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2002 Najeriya ta sha kaye ne a hannun Ajantina da 1-0 inda Gabriel Batistuta ya ci Najeriya kwallo daya.

A gasar cin kofin duniya da aka buga a shekarar 2010 kuma Ajantina ta doke Najeriya da ci daya da nema inda Gabriel Heinze ya ci Najeriya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu tsaron bayan Najeriya na yanzu suna da 'rowar kwallo'

Sai dai Najeriya ta samu galaba a kan Ajantina wani wasan sada zumuncin da suka buga a Abuja a watan Yunin shekarar 2011 da ci 4-1.

Amman Ajantina ta dauki fansa a watan Satumbar shekarar 2011 din da ci 3-1 a wasan sada zumuncin da suka yi a Dhaka.

Nasarar da Ajantina ta samu kan Najeria a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 ne ta sa jumullar nasarorinta kan Najeriya ta kai biyar, kuma ta yi canjaras sau daya inda Najeriya ta yi nasara a kanta sau daya.

Sai dai a wasa daya ne kawai Lionel Messi ya ci Najeriya cikin wadannan wasannin.

Labarai masu alaka