Man United ta samu fam miliyan 141

Man United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption United tana ta biyu a kan teburin Premier, bayan wasa 11 da ta buga a gasar

Manchester United ta sanar da samun kudin shiga da ya kai fam miliyan 141 a wata ukun farko, amma albashin da take biyan 'yan wasa ya karu sakamakon buga gasar Zakarun Turai da take yi.

A watan Janairu ne United ta zama ta daya a duniya wajen arziki a tsakanin kungiyoyin tamaula a karon farko a kididdigar da Deloitee ta fitar, rabon da ta taka wannan matsayin tun 2005.

A rahoton kudin da United ta sanar ta samu a ranar Alhamis a farkon wata uku zuwa karshen watan Satumbar 2017, ta samu karin fam miliyan 120.2 daidai da yadda ta samu a bara.

United ta kashe kusan fam miliyan 145 a farkon kakar bana wajen sayo sabbin 'yan wasa da suka hada da Romelu Lukaku daga Everton da Nemanja Matic daga Chelsea da kuma Victor Lindelof daga Benfica.

Haka kuma bashin da ake bin kungiyar ya kai fam miliyan 268 zuwa karshen Satumbar 2017, sai dai kuma ya ragu kenan zuwa fam miliyan 69.6.

United ta ci wasa hudu da ta yi a gasar cin kofin Zakarun Turai sannan ta kai daf da na kusa da karshe a kofin Carabao, sannan tana ta biyu a gasar cin kofin Premier.

Labarai masu alaka