Arsenal za ta kara da Tottenham

Premier Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal tana ta shida a kan teburin Premier, ita kuwa Tottenham tana ta uku a kan teburin

Kungiyar Arsenal za ta karbi bakuncin Tottenham a gasar Premier wasan mako na 12 da za su fafata a ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal tana mataki na shida a kan teburin Premier da maki 19, ita kuwa Tottenham tana ta uku a kan teburin da maki 23.

Kungiyoyin biyu sun kara sau biyu a bara, inda a Emirates suka tashi 1-1 a ranar 6 ga watan Nuwambar 2016, Tottenham ta ci wasa na biyu 2-0 a ranar 30 ga watan Afirilun 2017.

Arsenal za ta ziyarci Burnley a wasan mako na 13 a ranar 26 ga watan Nuwamba, ita kuwa Tottenham za ta karbi bakuncin West Bromwich Albion a ranar 25 ga watan na Nuwamba.

Tottenham ta kai wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai, yayin da Arsenal ta kai wasannin gaba a gasar Kofin Zakarun Turai amma ta Europa.

Labarai masu alaka