Dortmund ta dakatar da Aubameyang

Dortmund Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pierre-Emerick Aubameyang ya ci kwallo 31 a wasa 32 a gasar Bundesliga da ya buga a bara

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang a matakin da ta dauka na ladabtar da shi.

Dan wasan tawagar kwallon kafar Gabon ba zai buga wa Dortmund wasan Bundesliga da za ta fafata da VFB Stuttgart a ranar Juma'a ba.

Dortmund ta sanar da dakatar da dan kwallon mai shekara 28 bisa mayar wa da wani magoyin baya martani da ya yi tambaya a shafin sada zumunta na Twitter, amma kungiyar ba ta fayyace komai ba.

A bara ma sai da Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang, bayan da ya je Italiya ba tare da sanin kungiyar ba.

Wasa ya fara juya wa Dortmund baya, inda ta yi rashin nasara a fafatawa uku daga hudu da ta yi kwanan nan a Bundesliga ta kuma koma ta uku a kan teburin gasar bana.

Labarai masu alaka