Chelsea ta ci West Brom a ruwan sanyi

Premier Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Chelsea ta ci wasa 16 idan har Eden Hazard ya ci kwallo tun bayan da Antonio Conte ya zama kocin Chelsea

Chelsea ta casa West Bromwich Albion 4-0 a wasan mako na 12 a gasar Premier da suka kara a ranar Asabar.

Morata ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, sai Eden Hazard da ya ci na biyu, sannan Alonso ya ci ta uku kafin a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Eden Hazard ya ci ta hudu kuma ta biyu a karawar.

Chelsea ta hada maki 25 a wasa 12 da ta buga a gasar, ita kuwa West Brom tana nan da makinta 10.

Chelsea za ta ziyarci Liverpool a wasan mako na 13 a gasar ta Premier, ita kuwa West Brom za ta fafata da Tottenham a Wembley.

Labarai masu alaka