Sunderland ta dauki kociyan Wales Coleman

Chris Coleman Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chris Coleman ya karbi aikin kociyan Sunderland domin ceto ta daga halin da take ciki na rashin katabus

Kungiyar Sunderland da ke fama a gasar kasa da Premier, ta Championship ta nada Chris Coleman a matsayin kociyanta bayan da ya ajiye aikin horar da tawagar Wales.

Kociyan mai shekara 47, ya kulla yarjejeniyar shekara biyu da rabi da kungiyar, inda ya maye gurbin Simon Grayson, wanda aka kora a karshen watan Oktoba bayan wasa 18 da ya jagorance ta.

Sunderland din wadda ta fadi daga Premier a kakar da ta wuce, ita ce ta karshe a tebur bayan wasa daya kawai da ta ci a cikin 17 da ta yi.

Coleman wanda dan yankin Wales ne ya zama kociyanta na dindindin na goma tun bayan tafiyar Roy Keane a watan Disamba na 2008.

Wasansa na farko a kungiyar zai kasance a gidan Aston Villa ranar Talata.

Wasan da ta yi a gida 2-2 da Millwall ranar Asabar ya sa ta zama kungiyar kwallon kafa ta farko a Ingila da ta kasa nasara a wasa 20 na gida a jere, a duk wata gasa.

Coleman ya yi ritaya daga taka leda a Fulham a 2002, amma ya zauna a matsayin daya daga cikin jami'an aikin horar da 'yan wasan.

Ya maye gurbin kociyanta Jean Tigana a watan Afrilu na 2003 a matsayin wucin-gadi, inda ya ceto ta daga faduwa daga Premier, daga nan aka bas shi matsayin dindindin.

Ya jagoranci kungiyar zuwa matsayi na tara a Premier a kakarsa ta farko, amma daga karshe aka kore shi a Afrilun 2007.

Ya yi aiki da Real Sociedad da Coventry City da Athlitiki Enosi Larissa ta Girka, kafin a ba shi aikin horar da tawagar Wales a Janairun 2012, wata biyu bayan mutuwar Gary Speed.

Tsohon dan wasan na baya, Coleman ya kai Wales wasan kusa da karshe na kofin Turai na Euro 2016, amma ya koma Sunderland bayan da Wales ta kasa samun gurbin zuwa gasar kofin Duniya ta 2018