Kofin Confederation : TP Mazembe ta doke SuperSport 2-1

TP Mazembe lokacin da ta dauki kofin na Confederation Hakkin mallakar hoto Others
Image caption TP Mazembe na kan hanyar zama kungiya ta biyu da ta taba samun nasarar kare kofin na zakarun kungiyoyin Afirka

Zakarun gasar kofin Confederation na kungiyoyin Afirka TP Mazembe na Congo sun kama hanyar sake rike kofin bayan da suka doke SuperSport na Afirka ta Kudu a wasan karshe na karon farko da ci 2-1 a ranar Lahadi.

Masu rike da kofin ne suka fara daga ragar bakin nasu, a karawar da aka yi a birnin Lubumbashi, ta hannun dan wasansu na kasar Mali Adama Traore, minti 18 da shiga fili.

Bayan an dawo fafatawa daga hutun rabin lokaci ne, sai Sipho Percevale Mbule, dan Afirka ta Kudu ya farke wa bakin a minti na 47, amma kuma can a minti na 67 Daniel Adjei dan kasar Ghana ya kara daga ragar bakin.

A ranar Asabar mai zuwa ne za a yi karo na biyu na wasan a Afirka ta Kudu, inda kungiyar SuperSport din ta birnin Pretoria za ta karbi bakunci.

Kungiyar ta SuperSport ita ce ta biyu a Afirka ta Kudu gaba daya da ta taba zuwa wasan karshe na gasar ta kofin na Confederation, bayan Orlando Pirates, wadda Etoile du Sahel ta Tunisia ta doke ta a shekara ta 2015.

Kungiyar CS Sfaxien ta Tunisia ita ce kadai da ta taba nasarar kare kofin na Confederation a shekarar 2007 da 2008.

Sai kuma a yanzu da Zakarun na Afirka sau biyar TP Mazembe, da suka kama hanyar sake rike kofin, idan suka dace a haduwarsu ta biyu da kungiyar ta SuperSport United.

Kungiyar da ta yi nasarar daukar kofin na Confederation, mafi daraja na biyu a kofunan Zakarun Afirka, za ta karbi zunzurutun ladan kudi har dala miliyan 1,250,000.