West Brom ta kori kociyanta Tony Pulis

Tony Pulis Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Tony Pulis ne kociya na biyar da wata babbar kungiyar Ingila ta kora tun watan Agusta

An kori Tony Pulis daga aikin horar da West Brom bayan da kungiyar ta kasance maki daya kawai tsakaninta da rukunin masu faduwa daga gasar Premier, kuma ba tare da ta yi nasara ba a manyan wasanni goma.

A ranar Asabar ne Chelsea ta bi ta har gida ta doke ta da ci 4-0 a wasan mako na 12 na gasar ta Premier.

Kungiyar ta Albion ta ci wasanta uku na farkon kakar nan, sannan ta yi canjaras a hudu, ta kuma sha kashi a guda bakwai.

Tsohon kociyan West Brom din wanda ke wa Pulis mataimaki zai karbi aikin a matsayin riko, har zuwa wani lokaci nan gaba.

Shugaban kungiyar John Williams ya ce sun dauki wannan mataki ne domin amfanin kungiyar, saboda burinsu na samun sakamako mai kyau, abin ya zama sai takaici.

A ranar Asabar mai zuwa West Brom din za ta kara da Tottenham a wasan Premier a filin Wembley, sannan a gida za ta fafata da Newcastle a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, sai kuma ta kara da Crystal Palace, ranar Asbar 2 ga watan Disamba.

Alkaluman korar masu horar da 'yan wasa na Premier a bana;

Pulis ya kasance kociya na biyar da aka kora a gasar ta Premier a kakar bana. A watan Satumba, Crystal Palace ta sallami Frank de Boer bayan kwana 77 kawai a kungiyar, sannan Craig Shakespeare ya bar Leicester wata hudu kacal bayan ya kulla yarjejeniyar shekara uku da ita a a watan Oktoba.

Sai kuma Everton wadda ta watan na Oktoba ita ma ta kori Ronald Koeman, yayin da West Ham ta raba gari da Slaven Bilic a watan nan na Nuwamba.