Damben Boksin: An dage sake karon David Haye da Tony Bellew

Karawar David Haye (na hagu ) da Tony Bellew a watan Maris Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi wa David Haye (na hagu) tiyata a agara bayan da Tony Bellew ya doke shi a watan Maris

An dage ranar da za a sake damben boksin na David Haye da Tony Bellew, bayan da Haye ya zame a matattakalar bene ya ji rauni a lokacin da yake atisaye.

Haye wanda ke ajin babban nauyi, wanda kuma aka yi wa tiyata a kwanjinsa saboda raunin da ya ji, a ranar 16 ga watan nan na Nuwamba, ya ce lamarin ya bata masa rai matuka.

Tsohon zakaran damben boksin din ya fitar da wani sako, wanda a ciki yake bayar da hakuri ga abokin karawar tasa Tony, da iyalansa da masu horar da shi, da kuma magoya bayansu, wadanda ya ce ya san abin zai ba su takaici.

Zakaran damben ajin matsakaita nauyi na duniya, wanda shi ma dan Birtaniya ne, Bellew mai shekara 34, ya doke tsohon zakaran ajin babban nauyin na boksin din na duniya, Haye, mai shekara 37, a turmi na 11 a karawar da suka yi a watan Maris.

Damben na biyu wanda aka shirya da za a yi ranar 17 ga watan Disamba a filin wasa na O2 Arena da ke Landan, yanzu za a yi shi ne ranar 24 ga watan Maris ko ranar biyar ga watan Mayu na 2018.