Tennis: Gwarzuwar Wimbledon, Novotna ta rasu

Jana Novotna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kukan Novotna na rashin nasara cin gasar Wimbledon a 1993, ya zama na nasara a 1998

Tsohuwar gwarzuwar gasar tennis ta Wimbledon Jana Novotna, 'yar kasar Czech ta rasu sakamakon cutar daji, tana da shekara 49.

Hukumar kwallon tennis ta mata ta duniya wadda ta bayar da sanarwar rasuwar ta ce, Novotna, ta rasu ne cikin kwanciyar hankali iyalinta na kewaye da ita.

A shekarar 1993 da 1997 ne Novotna ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar ta Wimbledon, kafin daga karshe ta yi nasara a gasar bayan ta doke Nathalie Tauziat a 1998.

'Yar wasan ta shiga ran 'yan kallo ne lokacin da ta fashe da kuka bayan da ta yi rashin nasara a hannun gwana 'yar Jamus, Steffi Graf a 1993, a wasan na karshe, wanda hakan ya sa har Gimbiya Katherine ta gidan Sarautar Birtaniya ta rika rarrashinta.

Bayan kofin nata daya na Wimbledon, ta ci manyan kofuna na duniya 12 na gasar 'yan bibbiyu da kuma wasu guda hudu.

Haka kuma an shigar da ita cikin jerin gwanayen kwallon tennis na duniya a 2005.