Hukuncin farko zai hau kan Oumar Niasse na Everton kan yaudarar alkalin wasa

Oumar Niasse bayan ya rama kwallo ta biyu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bayan samun fanaretin Oumar Niasse ya kuma farke kwallo ta biyu a wasan da suka yi canjaras 2-2 da Crystal Palace

Dan wasan gaba na Everton Oumar Niasse ya zama na farko a gasar Premier da hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta tuhuma kan yaudarar alkalin wasa ya fadi da gangan har aka bayar da fanareti.

Dan wasan na tawagar Senegal ya yi nasarar samun fanareti ne wadda aka yi takaddama a kanta, bayan da aka ga kamar Scott Dann, na Crystal Palace ya yi masa keta a wasan da suka yi canjaras 2-2 ranar Asabar, fanaretin da Leighton Baines ya ci.

Bayan nan ne kuma Niasse ya farke wa kungiyar tasa bal ta biyu a wasan da aka yi a gidan Crystal Palace, Selhurst Park.

Hukumar kwallon kafa ta ba shi wa'adin zuwa karfe shida agogon GMT ya bayar da bahasi kan zargin da ake masa na yaudarar.

A watan Mayu ne aka bullo da sabuwar dokar da ta ba da damar tuhumar dan wasa bayan wasa a kan faduduwa da gangan domin yaudarar alkalin wasa, ya ba su fanareti ko wani abu.

Dan wasan gaba na kungiyar Carlisle Shaun Miller shi ne na farko da aka haramta wa buga wasa biyu a watan Oktoba a kan irin wannan laifi.

A farkon watan nan aka dakatar da dan wasan baya na Bristol City Bailey Wright wasa biyu bayan da aka same shi da laifin faduwa da ganagan din domin yaudarar alkalin wasa.

Ya fadi ne da gangan a wata haduwa da suka yi da dan wasan Fulham Aboubakar Kamara, ba tare da kwallo ba, an kuma soke katin korar da alkalin wasa ya ba wa Kamar kan lamarin.