Fifa ta hukunta wasu tsoffin shugabannin hukumomin kwallon kafa

Rafael Esquivel na Venezuela (a hagu) da Julio Rocha na Nicaraguwa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rafael Esquivel na Venezuela (a hagu) da Julio Rocha na Nicaragua dukkaninsu an haramta musu shiga harkokin kwallon kafa har abada a kan rashawa

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta haramta wa tsoffin shugabannin hukumomin kwallon kafa na kasashen Guam da Nicaragua da Venezuela shiga harkokin wasan har karshen rayuwarsu, bisa laifukan rashawa.

Fifa ta haramta wa Richard Lai na Guam da Rafael Esquivel na Venezuela da kuma Julio Rocha na Nicaragua shiga duk wasu harkokin wasan kwallon kafa har abada.

Hukumar ta kwallon kafar ta duniya ta fara binciken Lai ne bayan da ya amsa laifin aikta zamba a Amurka a watan Afrilu.

Haka su ma sauran takwarorin nasa biyu Esquivel da Rocha sun amsa tuhumar da aka yi musu kan rashawa a watan Mayu na 2015.

Dukkanin laifukan dai sun danganci bayar da kwangilar damar nuna wasanni ta talabijin da rediyo da kuma tallace-tallace na wasannin.

Dukkanin mutanen uku bayan kasancewarsu tsoffin shugabannin hukumomin kwallon kafa na kasashensu, sun kuma rike mukamai a hukumar kwallon kafar ta duniya.

Tuhumar ta Lai ta shafi Sheikh Ahmad Al-Fahad Al-Sabah, wanda bangaren shari'a na Fifa bai fito fili karara ya ambace shi ba a lamarin.

Amma kuma takardun kotu sun bayyana karara cewa shi ne sila ko hanyar cin hancin da aka ba wa Lai na neman goyon baya a zaben shugabancin hukumar kwalllon kafa ta Asia da kuma ta duniya.

Kwanaki kadan bayan da Lai ya amsa laifinsa ne Sheikh Al-Sabah, dan Kuwait ya sauka daga mukamansa na harkokin kwallon kafa, ciki har da kujerarsa a majalisar zartarwar Fifa.