Yakubu Aiyegbeni ya yi ritaya daga kwallon kafa

Yakubu Aiyegbeni Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption Yakubu yana daya daga cikin matasan 'yan wasa da suka ci kwallo uku rigis a wasa daya na gasar zakarun Turai

Tsohon dan wasan Najeriya da wasu kungiyoyin Ingila musamman Premier Yakubu Aiyegbeni, ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa yana da shekara 35.

A kusan shekara goma da ya shafe a kungiyoyin kwallon kafa na Ingila, tsakanin watan Janairu na shekara ta 2003 da watan Yuni na 2012, Yakubu, wanda ake wa lakabi da Yak, ya ci kwallo 114 a wasannin lig 293 da ya yi yawanci a Premier.

Kididdiga ta nuna kusan ya rika cin kwallo akalla daya a duk lokacin da ya buga wa Portsmouth da Middlesbrough da Everton da Leicester da kuma Blackburn kafin ya koma kungiyar Guangzhou ta kasar China.

Daga baya ya sake dawowa Ingila inda ya taka leda na wani dan lokaci a kungiyar Reading a 2015, kafin ya koma Coventry City.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lokacin da Yakubu ya barar wa da Najeriya damar cin Koriya ta Kudu

Yakubu ya yi wa tawagar Najeriya wasa a gasar cin kofin duniya ta 2010, inda ya barar wa da kasar wata kyakkyawar dama ta cin kwallo a karawarsu da Koriya ta Kudu.