Kocin Chelsea Antonio Conte ya nemi taimakon 'yan jarida

Willian na Chelsea ya taka rawar-gani a wasan da Qarabag Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasa na 200 ke nan da Willian ya buga wa Chelsea wadda ta kai zagayen sili-daya-kwale a gasar zakarun Turai sau 14 a cikin 15 da ta je

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya bukaci 'yan jarida da su taimaka su nuna irin rashin dacewar da yake ganin an yi a tsarin wasannin kungiyarsa, bayan sun lallasa Qarabag da ci 4-0 a gasar zakarun Turai.

Bayan wasan ne Conte ya bayyana damuwarsa ta yadda za su yi wasa da Liverpool a Premier ranar Asabar, kwana biyu bayan doguwar tafiyar da suka yi ta mil 5,000 zuwa Azerbaijan, kasar Qarabag.

Chelsea ta yi fama da irin wannan matsala a tsakanin wasanta da Atletico Madrid da kuma Manchester City a watan Satumba.

Kociyan dan Italiya wanda kungiyarsa ke matsayi na uku a teburin Premier da maki biyu a gaban Liverpool, ya ce ya kamata 'yan jarida su nuna wa duniya saboda wannan bakon abu ne.

Willian ya ci kwallo biyu yayin da Chelsean ta tsallaka zuwa mataki na gaba na kungiyoyi 16 a gasar ta zakarun Turai.

Kafin wasan Willian ya ci bal daya ne kawai a kakar nan a haduwarsu da Everton a Premier - amma kuma ya taka muhimmiyar rawa a wannan nasara da Chelsea ta yi, inda ya samar musu fanareti biyu.

Alkalin wasa ya ba wa Chelsea fanareti lokacin da yake ganin dan bayan Qarabag Rashad Sadygov ya kayar da Willian. Lafirin ya kuma ba wa Sadygov jan kati (na kora), kafin Eden Hazard ya buga fanaretin ya ci a minti na 21.

Chelsea ta kara ta biyu bayan wani wasan ba-ni-in-ba-ka da aka yi daga Fabregas zuwa Willian, wanda ya ba wa Hazard, shi kuma ya mayar wa Willian din ya jefa ta a raga a minti na 36.

Bayan wata ketar da aka sake yi wa Willian alkalin wasa ya ba Chelsea fanareti, wadda fabregas ya buga ya ci a minti na 73, duk da cewa da farko ya buga ya ci amma lafirin ya ce ya sake.

A minti na 85 kuma Willian ya samu wata dama inda ya kwararo wata kwallo, wadda ba ta zame ko ina ba sai a ragar Qarabag, wanda hakan ya tabbatar wa Chelsea tafiya mataki na gaba da ragowar wasa daya.

Yanzu Chelsea ce ta daya a rukuninsu na uku, Group C da maki 10, yayin da Roma ke bi mata baya da maki takwas, duk da ci 2-0 da Atletico Madrid ta uku mai maki shida ta yi mata a Spaniya.

Chelsea wadda ita ce kungiyar Ingila ta karshe da ta dauki kofin zakarun Turai a 2012, ta doke Qarabag ta karshe a rukunin mai maki 2, a haduwarsu ta farko a gasar 6-0 a Stamford Bridge, a watan satumba.