Gwanayen Fifa: Jamus ta daya a duniya, Senegal a Afirka

'Yan wasan Senegal na murna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Senegal ba ta taba samun cigaba ba a jerin sunayen na Fifa kamar na yanzu, inda ta tashi daga ta 32 zuwa ta 23

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta fitar da jerin sunayen wannan watan na kasashen da suka yi fice a wasan a duniya, inda Jamus ke zaman ta daya, Brazil na bi mata baya, yayin da Senegal ta 23 ke zaman ta daya a Afirka.

Wannan cigaba na Kungiyar ta Teranga Lions ta Senegal ya kasance ne sakamakon nasarar da ta yi sau biyu a kan Afrika ta Kudu a watan Nuwamba, abin da ya ba ta damar zuwa gasar kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa a Rasha

Ga jerin sunayen;

1. Germany 2. Brazil 3. Portugal 4. Argentina 5. Belgium 6. Spain 7. Poland 8. Switzerland 9. France 10. Chile 11. Peru 12.Denmark 13. Colombia 14. Italy 15. Englang

Duk da cewa Italiya ba ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa ba a Rasha, ta wuce Ingila.

Tunisia ce ta 27 a duniya yayin da take ta biyu a Afirka, sai Masar ta uku a Afirka amma ta 31 a duniya. Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo tana ta hudu a Afirka kuma ta 36 a duniya.

Sai Morocco tana matsayi na biyar a Afirka amma ta 40 a duniya, Burkina Faso na bi mata baya a Afirka amma ta 44 a duniya.

Kasar kamaru ta kasance ta bakwai a nahiyar Afirka yayin da take ta 45 a gaba daya. Sai kuma Najeriya wadda ke matsayi na takwas a Afirka, kuma ta 50 a duniya, wadda kuma ta kasance mafi koma baya a cikin kasashen Afirka da za su je gasar kofin duniya a Rasha.