Fyade: An yanke wa Robinho hukuncin zaman yari na shekara 9

Robin a lokacin yana AC Milan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Robinho mai shekara 33 wanda bai je kotun ba ya musanta zargin

Wata kotu a Italiya ta samu tsohon dan wasan Brazil Robinho da laifin fyade,kuma ta yanke masa zaman gidan yari na shekara tara.

Kotun ta ce lamarin ya faru ne shekara hudu da ta wuce, lokacin da Robinho din yake wasa a kungiyar AC Milan, inda dan wasan da shi da wasu 'yan Brazil mutum biyar suka bugar da matar mai shekara 22, yar kasar Albaniya, sannan suka yi mata fyade.

Bisa tsarin shari'a na kasar ta Italiya ba za a aiwatar da hukuncin ba har sai an yi ta daukaka kara, zuwa matakin karshe.

Robinhon wanda ya yi wa kasarsa Brazil wasa 100 bai je kotun ba kuma ya musanta zargin ta hannun lauyansa. Bayan AC Milan Robinho ya kuma yi wasa a Real Madrid da Manchester City sannan ya tafi China, kafin kuma yanzu ya koma wasa a Atletico Mineiro ta Brazil.