Premier: Southampton ta caskara Everton 4-1

Lokacin gumurzun Everton da Southampton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Southampton ta koma ta 10 damaki 16 a tebur bayan casa Everton wadda ita kuma ta zama ta 16 da maki 12

Everton ta ci gaba da shiga tsaka-mai-wuya a karkashin kociyan rikon-kwarya David Unsworth bayan da ta sha kashi 4-1 a gidan Southampton a wasan Premier na mako na 13.

Dusan Tadic ne ya fara ci wa masu masaukin bakin a minti na 18, amma ana dab da tafiya hutun rabin lokaci sai Sigurdsson ya farke wa Everton, wadda a yanzu wasa daya kawai ta ci a cikin bakwai a karkashin jagorancin Unsworth.

Bayan an dawo ne sai dan wasan gaba na Southampton Charlie Austin ya zura kwalllo biyu a minti na 52 da kuma minti na 58, kafin kuma can ana dab da tashi a minti na 87 Steven Davis ya ci ta karshe.

Wannan rashin nasara ya zo wa Everton ne kwana uku bayan casa ta 5-1 da Atalanta ta yi a gasar kofin zakarun Turai ta Europa, lamarin da ya sa tsohon dan wasan kungiyar Gary Lineker ya bayyana ta da shirme.

A yanzu an zura wa Everton kwallo 28 bayan wasa 13 a gasar Premier ta bana, abin da ba a taba yi musu ba tun kakar 1958-59.

Nasara daya kacal da suka yi a karkashin jagorancin Unsworth ita ce ta ranar biyar ga watan Nuwamba a kan Watford, wadda Everton din ke neman daukar kociyanta Marco Silva.