Arsenal ta farfado a wasan waje, da nasara kan Burnley 1-0

Dan wasan baya na Burnley James Tarkowski lokacin da ya ture Aaron Ramsey Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan baya na Burnley James Tarkowski lokacin da ya ture Aaron Ramsey alkalin wasa Lee Mason ya ba wa Arsenal fanareti

Arsenal ta ci gaba da yin manyan wasanninta har zuwa goma ba tare da an doke ta ba, inda ta buge Burnley da ci 1-0 a wasan Premier na 13, da nasara a 7, da canjaras a 3.

Wasan ya kasance kamar maimaici na haduwarsu ta bara a gidan Arsenal, Emirates, lokacin da Alexis Sanchez ya ci fanaretin da suka samu a minti na 98.

Haka kuma wannan shi ne karo na uku a jere wanda Arsenal take cin kwallon da ta ba ta nasara a kan Burnley a daidai lokacin tashi.

A yanzu Burnley ta yi rashin nasara a wasanninta na Premier uku a gida da Arsenal 1-0.

Kafin wasan Arsenal ta samu maki hudu ne kawai a waje a bana, kuma rashin kokarinsu a wasan wajen kamar zai ci gaba kafin Sanchez ya ceto su.

Da wannan cin Sanchez ya ci kwallo hudu a wasa biyar da ya buga na Premier da Burnley, ya ci Sunderland 6 Hull kuma 7.

Yanzu Arsenal ta hau mataki na hudu a tebur da maki 25, a gaban abokiyar hamayyarta ta Landan, Tottenham mai maki 24, wadda ta yi kunnen doki 1-1 da West Brom ranar Asabar, yayin da Burnley take matsayi na 7 da maki 22.

A wasan gaba Arsenal za ta karbi bakuncin Huddersfield, ita kuwa Burnley za ta je gidan Bournemouth ranar Laraba (dukkaninsu da karfe 19:54 GMT).