AC Milan ta kori kociyanta Montella, ta nada Gattuso

Vincenzo Montella korarren kociyan AC Milan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Yuni na 2016 Vincenzo Montella ya fara aikin kociyan AC Milan

AC Milan ta kori kociyanta Vincenzo Montella sannan ta maye gurbinsa da Gennaro Gattuso bayan ya kasa tabuka abin-a-zo-a-gani a kungiyar.

Kungiyar tana matsayi na bakwai ne a teburin Serie A da maki 20, 18 tsakaninta da ta daya Napoli, bayan nasara biyu kawai a wasa tara na gasar.

A ranar Lahadi ne ta yi canjaras 0-0 da Torino a gida, kuma ta yi rashin nasara a shida daga cikin manyan wasanninta 14 a kakar bana.

Shi dai kociyan na yanzu, Gattuso wanda tsohon dan wasan kungiyar ta AC Milan ne an ciyar da shi gaba ne daga matsayin kociyan karamar kungiyar.

Kociyan mai shekara 39, dan Italiya ya yi wa Milan wasa tsakanin 1999 da 2013, inda ya dauki kofin gasar Serie A da na zakarun Turai sau bibbiyu.

A ranar Talata ne zai bayyana a wani taron manema labarai a filin atisayen kungiyar, Milanello.

Bayan korar tasa Montella ya sanya wata sanarwa a shafukan sada zumunta da muhawara, wadda a ciki yake nuna godiya da cewa ba karamar martaba ba ce kasancewarsa kociyan kungiyar.

AC Milan wadda ta dauki kofin Serie A sau 18 kuma ta dauki kofin zakarun Turai sau bakwai, ba ta samu shiga cikin manyan kungiyoyi uku ba na gasar tun 2013.

Kungiyar ta kashe fam miliyan 205 wurin sayen sabbin 'yan wasa tun lokacin da attajiri dan kasuwar China Li Yonghong ya sayi kungiyar a watan Afrilu na shekarar da ta wuce.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna godiyarta ga tsohon kociyan Mista Montella tare da dukkanin jami'ansa.