Gareth Bale zai yi wasa ranar Talata - Zidane

Gareth Bale na Real Madrid da Wales Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale ya dauki kofin zakarun Turai uku da Real Madrid

Dan wasan Real Madrid Gareth Bale zai taka leda ranar Talata a karon farko a cikin wata biyu in ji kociyan kungiyar ta Spaniya Zinedine Zidane.

Da farko Bale ya ji rauni ne a guiwarsa kafin kuma daga baya ya kara jin wani ciwon a cinya, amma yanzu tun da ya warke zai buga wasan da za su yi da kungiyar Fuenlebrada ta rukuni na uku a kasar a gasar Copa del Rey.

Dan wasan gaban na Wales mai shekara, 28, bai taka leda ba tun lokacin da Real Madrid ta bi Borussia Dortmund har gida ta doke ta 3-1 ranar 26 ga watan Satumba.

Bale, wanda bai samu damar buga wasannin karshe na neman zuwa gasar kofin duniya na Wales ba, takitin da suka rasa, bai yi wani wasa ko daya tare da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema a wata fafatawa ta Real Madrid ba, saboda ko dai wani ya ji rauni ko kuma hukuncin hana buga wasa na kan wani daga cikinsu.

Zidane ya ce yana matukar sha'awar ya ga 'yan wasan uku, Gareth da Cristiano da Karim, suna taka leda tare.

Bale ya ci kwallo 70 a wasa 159 da ya yi wa Real, inda ya ci kofin zakarun Turai uku da kuma kofin La Liga na bara.