Alexis Sanchez da Mesut Ozil ba za su tafi a watan Janairu ba - Wenger

Alexis Sanchez and Mesut Ozil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alexis Sanchez da Mesut Ozil sun ci wa Arsenal kwallaye 149

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, yana tsammanin dan wasan gaba Alexis Sanchez da kuma dan wasan tsakiya Mesut Ozil za su tsaya a kulob din a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairun 2018.

Yarjejeniyoyin 'yan wasan biyu za su kare ne a karshen wannan kakar.

Da aka tambaye shi cewa ko yana tunanin 'yan wasan biyu za su tsaya a kulob din, Wenger ya ce: "E, kwarai."

Dan Faransan ya kuma ce dan wasan tsakiyar Ingila, Jack Wilshere, yana bukatar ya ci gaba da zama a Gunners.

Wenger ya kara da cewa: "Zan yi kokarin ganin ya zauna a nan domin shi wani kwararren dan wasa ne."

Dan wasan tsakiyar Ingilar, mai shekara 25, yana fama da raunuka tun lokacin da ya fara taka wa Gunners leda a shekarar 2008, kuma ya je buga wasa aro a Bournemouth a kakar shekarar 2016 zuwa ta 2017.

Labarai masu alaka

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba