Ya kamata a hukunta Lukaku - Ian Wright

Romelu Lukaku Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallo daya kawai Romelu Lukaku ya ci wa Manchester United a wasansa 10 na baya bayan nan

Ya kamata a ce an haramta wa dan wasan gaba na manchester United Romelu Lukaku buga wasanni saboda dukan da ya yi wa dan bayan Brighton Gaetan Bong in ji mai yi wa BBC fashin baki Ian Wright.

Lamarin ya faru ne a wasan Premier wanda Manchester United ta doke Brighton 1-0, ranar Asabar, amma kuma alkalin wasa Neil Swarbrick, bai gani ba a lokacin.

Bayan da wani kwamitin bincike na hukumar kwallon kafa ta Ingila ya yi nazari a kai ya ce babu bukatar yin wani hukunci.

Ian Wright, tsohon dan wasan Arsenal da Ingila ya ce, yana ganin abin a lokacin ya yi tunanin cewa kila za a yi nazari a kai. Sai ka yi tunanin me ya sa ba a hukunta shi ba?

Tsohon dan wasan ya ce akwai cikakkiyar sheda da ya kamata a hukunta shi, domin ya haure shi har sau biyu, amma bai san dalilin da ya sa aka kyale shi ba.