Tsohon matashin dan wasan Man United John Cofie ya koma Derry City

John Cofie lokacin yana Manchester United Hakkin mallakar hoto Others
Image caption John Cofie ya ci wa Manchester United kwallo a gasar Milk Cup a 2010

Wani dan wasa da Manchester United ta taba saye fam miliyan daya lokacin yana shekara 14, zai taka leda a kungiyar Derry City da ke gasar lig din Ireland a kaka mai zuwa.

Dan wasan na Ingila haifaffe kuma dan asalin Ghana, John Cofie, wanda yanzu yake shekara 24, na daya daga cikin 'yan wasa biyar da kungiyar ta Ireland ta saya ranar Talata.

A shekara ta 2007 Manchester United ta kasa abokan hamayyarta a Premier, Liverpool da Chelsea a zawarcin matashin dan wasan wanda a lokacin yana Burnley.

Manchester United ta saye shi, sannan ya tafi Royal Antwerp, da Barnsley da kum Southport, in ji kocin Derry Kenny Shiels, wanda ya kara da cewa wannan wata dama ce ga dan wasan da zai farfado da sana'arsa.