Premier: Manchester United ta doke watford 4-2

Ashley Young lokacin da yake cin Watford Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ashley Young ya ci kwallo biyu a Premier a karon farko tun watan Maris na 2012

Ashley Young ya zura kwallo biyu a ragar tsohuwar kungiyarsa a wasan da Manchester United ta doke Watford 4-2 a wasan Premier na mako na 14.

United ta jure wa matsin masu masaukin nasu a kusan karshen wasan, wanda suka ci kwallo uku a cikin minti 13 a kashin farko na wasan, inda ta rage ratar da ke tsakaninta da ta daya a tebur Manchester City zuwa maki biyar.

Ko da yake kungiyar ta Pep Guardiola za ta iya sake ba su wannan tazara ta maki takwas, idan ta hadu da Southampton ranar Laraba.

Young ya afara cin ta farko ne minti 19 da shiga fili, bayan minti shida kuma ya kara ta biyu.

Bayan minti bakwai kuma sai Martial ya ci tasa wadda ita ce ta uku da manchester United din ta zura.

Can an nitsa zuwa minti 77 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci 'yan Watford sun matsa wa United, sai suka samu fanareti wadda Troy Deeney ya kadar da De Gea ya jefa ta a raga.

Daga nan ne kuma suka kara samun karfin guiwa suka kai wata kora da Abdoulaye Doucoure ya kara ci musu ta biyu a minti na 84.

Sai dai kuma minti biyu tsakani ne sai Lingard ya yi musu ta'annati ya ci wa United ta hudu wadda ta sanyaya jikin 'yan Watford din.

A ranar Asabar Watford ta takwas da maki 21, za ta kara karbar bakuncin Tottenham (lokaci15:00 GMT) yayin da Manchester United za ta je gidan Arsenal a wannan rana (lokaci 17:30 GMT).

Sauran wasannin Premier na ranar Talata;

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kwallon da Newcastle ta farke ta sa kocinsu Rafa Benitez bai taba shan kashi ba a duk kungiyar da ya jagoranta ta hadu da West Brom

West Brom Albion 2-2 Newcastle: Sakamakaon ya sa West Brom tana matsayi na 16 da maki 12, yayin da Newcastle take ta 12 da maki 15

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Christian Benteke a fara wasa a karon farko a Crystal Palace tunkarshen watan Satumba

Brighton 0-0 Crystal Palace: Brighton tana matsayi na 10 da maki 17, bakinta 'yan Newcastle suna na karshe a tebur (20) da maki tara.