Premier: Leicester ta yi wa Tottenham bazata da 2-1

Jamie Vardy lokacin da yake cin Tottenham Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cin da Jamie Vardy ya yi shi ne na 100 a gasarsa ta lig

Tottenham ta kasa amfani da tarin damar da ta samu a wasan da mai masaukinta Leicester ta doke ta da ci 2-1, har ta dago zuwa tsakiyar tebur, a matsayin ta 9 da maki 17.

Jamie Vardy ne ya fara ci wa Leicester kwallo a minti na 13, kafin kuma Riyad Mahrez ya ci ta biyu ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Saura minti 12 a tashi daga wasa ne sai dodon-ragar 'yan Tottenham harry kane ya farke kwallo daya, bayan da Christian Eriksen ya barar da wata dama.

Yayin da bakin suka tashi tsaye wajen rama ta biyu kafin alkalin wasa Anthony Taylor ya tashi Fernando Llorente shi ma ya barar da wata damar.

Yanzu Tottenham ta koma ta biyar a tebur da maki 24, bayan wasa 14 na gasar ta Premier