Copa del Rey: Real Madrid ta tsallake siradi 2-2 da Fuenlabrada

Gareth Bale lokacin da ya kai hari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gareth Bale ya ceci Real Madrid bayan dawowarsa daga jinya

Gareth Bale ya ceci Real Madrid a hannun 'yar karamar kungiya ta gasar mataki na uku ta Spaniya Fuenlabrada inda ya yi sanadin cin kwallo biyu bayan dawowarsa daga jinya, a gasar Copa del Rey.

Dan wasan gaban na Wales mai shekara, 28, wanda ya shafe wata biyu yana jinyar guiwa da cinya, ya shigo wasan ne daga baya, ya samar da kwallo biyu da Borja Mayoral ya ci suka yi canjaras a wasan na karawa ta biyu.

Luis Milla ne ya fara daga ragar kungiyar ta Zinedine Zidane 1-0 a minti na 25 a wasan na Santiago Bernabeu, kafin a sako Gareth Bale, wanda shigowarsa ya sauya lissafin a minti na 63, inda ya dauko wa Mayoral kwallo ta gefe ya farke da ka.

kafin daga bisani ana shirin tashi a minti na 89 Alvaro Portilla ya farke wa bakin matasan.

Kusan minti bakwai tsakani ne kuma sai Bale din ya sake kai wani hari, wanda mai tsaron ragar bakin ya amayar da kwallon, Mayoral bai yi wata-wata ba ya mayar da ita raga.

Haka aka tunkari lokacin karshen wasan kafin minti na 89 Alvaro Portilla ya farke wa bakin matasan.

Nasarar da Real ta yi 2-0 a haduwarsu ta farko ta ba wa zakarun kofin na Copa del Rey sau 19, damar wucewa zuwa matakin kungiyoyi 16, na sili-daya-kwale.