Sam Allardayce na dab da zama kocin Everton

Sam Allardyce (a tsakiya) da Jose Mourinho (a hagu) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sam Allardyce ya ce ba shi da wani buri na sake zama kociya bayan da ya bar Crystal Palace

Sam Allardyce zai kammala kulla yarjejeniyar zama kocin kungiyar Everton ta Premier a ranar Larabar nan, sakamakon fafutukar da take yi ta fita daga halin katabus da take ciki.

Tsohon kocin na Ingila mai shekara 63 zai zama magajin Ronald Koeman, wanda aka kora a watan Oktoba yayin da kungiyar ke matsayi na 18 a tebur.

David Unsworth wanda ke zaman kocin kungiyar na rikon kwarya shi ne zai jagorance ta a wasan da za ta je gidan West Ham, wato Goodison Park da karfe 8:00 na dare agogon GMT, a Larabar nan.

Ba wani aiki da Allardyce yake yi tun lokacin da ya ajiye aiki da Crystal Palace a watan Mayu.

Ya sauka ne bayan wata biyar kawai a kai, wanda shi ne aikinsa na farko tun bayan wasa daya da ya jagoranci Ingila, bayan da ya jagoranci kungiyar ta yi nasara a wasa takwas a cikin 21, ta kammala a matsayi na 14 a tebur.

Yanzu Everton tana ta 17 a tebur, kuma ta yi nasara a wasa daya ne kawai a cikin bakwai da ta yi na kowace gasa a karkashin jagorancin Unsworth, wanda shi ne kocin matasan kungiyar 'yan kasa da shekara 23.

Koeman dan Holland ya kai Everton matsayi na bakwai a tebur a kakarsa ta farko a kungiyar a bara, amma an kore shi kwana daya bayan da a gida Arsenal ta doke su da ci 5-2 a ranar 22 ga watan Oktoba.

Kungiyar ta kashe sama da fam miliyan 130 wajen sayen sabbin 'yan wasa, amma tana fama a yanzu ba tare da Romelu Lukaku ba, wanda ya fi ci mata kwallo a kakar da ta gabata, wanda Manchester United ta saya fam miliyan 75 a watan Yuli.