Abubuwan kara kuzari: Fifa ta wanke Rasha

Mrs Fatma Samoura ta maye gurbin tsohon sakatare janar na Fifa Jerome Valcke, wanda aka haramta wa shiga harkar kwallon kafa tsawon shekara 12 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Madam Fatma Samoura ta maye gurbin tsohon sakatare janar na Fifa Jerome Valcke, wanda aka haramta wa shiga harkar kwallon kafa tsawon shekara 12

Babbar Sakatariyar hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Fatma Samoura ta sheda wa BBC cewa babu badakalar amfani da abubuwan kara kuzari a harkar wasan kwallon kafa a Rasha.

Madam Samoura, wadda ta je birnin Moscow domin halartar zaman shirya jadawalin wasannin gasar kofin duniya da za a yi ranar Juma'a, ta kuma kare damar Rasha ta karbar bakuncin gasar ta kofin duniya.

Ta yi hakan ne duk da kwace lambobin bajinta na gasar Olympics na 'yan wasan Rashar saboda samunsu da laifin amfani da abubuwan kara kuzari, da kuma hadarin da take fuskanta na hana ta halartar gasar Olympic ta lokacin hutura a birnin PyeongChang, na Koriya ta Kudu.

Babbar Sakatariyar ta ce daga samfurin da aka dauka na jini da fitsari sama da 800 na 'yan wasan kwallon kafar babu wanda aka samu da yin amfani da abubuwan kara kuzari.

Amma ta ce da sun ga wani abu mai muhimmanci a gwaje-gwajen da ake yi nan da nan za su dauki mataki a kai.