David Silva ya tsawaita zamansa a Manchester City

David Silva Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Yanzu David Silva wanda ya yi wa City kyaftin a wasanta na zakarun Turai da Napoli a watan Oktoba, zai zauna a kungiyar har shekara 10 kenan,

David Silva ya sanya hannu a yarjejeniyar kara zamansa a Manchester City da shekara daya, ta yadda zai ci gaba da taka leda a kungiyar har zuwa shekara ta 2020.

Dan wasan mai shekara 31, na Spaniya ya koma City ne daga Valencia a kan kudi fam miliyan 24 a shekara ta 2010.

Dan wasan na tsakiya ya dauki kofin Premier biyu, da na FA daya da kuma na Lig guda biyu a zamansa a Man City.

Kungiyar ta Pep Guardiola ta bayar da tazarar maki takwas bayan nasara 12 a jere a gasar ta Premier.

Nasara ta baya bayan nan da ta yi ita ce wadda ta ci Southampton ana dakika 30 ta karshe a tashi daga wasansu ranar Laraba, bayan kara minti biyar na cikon bata lokaci, inda suka yi 2-1.

Silva wanda ya bayar da kwallo har sau takwas aka ci a kakar bana ya kasance na daya, domin ba wanda ya yi wannan kokarin zuwa yanzu a gasar ta Premier, kuma ya ce burinsa shi ne kara cin kofuna a Etihad.

Dan wasan ya yi wa City wasa 234 a gasar Premier tun lokacin da ya koma kungiyar daga Valencia a 2010, inda ya ci kwallo 40.