Aikin Koci: Ana nuna wa bakake da tsirarun jinsi wariya a Ingila

Jimmy Floyd Hasselbaink kocin Northampton Town Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Satumba aka nada Jimmy Floyd Hasselbaink a matsayin kocin Northampton Town

Koci-koci bakaken fata da kuma wadanda suka fito daga tsirarun jinsi har yanzu suna fuskantar matsalar nuna bambanci a wasan kwallon kafa na Ingila, kamar yadda wani rahoto na masana wasanni ya nuna.

Rahoton na shekara-shekara na kungiyar masana harkokin wasannin (SPTT), ya ce cigaban da aka samu na kawar da wannan matsala tun shekara ta 2014 kadan ne.

Binciken ya nuna cewa daga cikin manyan koci-koci 482, na manyan gasar kwallon kafa hudu na Ingila, 22 ne kawai bakaken fata da wadanda suka fito daga tsirarun jinsi.

Masu binciken suna son a bulla da tsarin da ake kira 'Rooney Rule', wanda aka yi wa lakabin da sunan tsohon mai kungiyar American Football, Dan Rooney, wanda hukumar kwallon zari ruga ta Amurka ta bullo da shi a 2003, wanda ya tanadi cewa dole ne a tantance akalla koci daya bakar fata ko wanda ya fito daga tsirarun jinsi a duk wani matsayi na babban koci da za a dauka.

An fitar da alkaluman ne bisa abin da ake da shi a farkon watan Satumba, wato kafin nadin Jimmy Floyd Hasselbaink a matsayin kocin Northampton da kuma Jack Lester a kungiyar Chesterfield.

Nadin nasu ya kawo yawan koci-koci bakaken fata ko 'yan tsirarun jinsi zuwa biyar a kungiyoyin 92.