Gasar gudun Landan: Eliud Kipchoge zai tashi tsaye kan Mo Farah

Eliud Kipchoge Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Eliud Kipchoge gwanin dan tseren kewaya fili ne kafin ya koma na titi

Zakaran gasar Olympic Eliud Kipchoge ya ce zai dauki kalubalan Mo Farah na shiga gasar gudun yada-kanin-wani na Landan da matukar muhimmanci.

Kipchoge, dan Kenya, mai shekara 33, shi ne ya cinye gasar ta London Marathon, a shekara ta 2015 da ta 2016, kuma zai sake shiga gasar a shekara mai zuwa ta 2018.

Farah ya shiga gasar ta Landan sau biyu, amma wannan da za a yi a Afrilu na shekara mai kamawa za ta kasance ta farko, tun bayan da ya sauya wasa daga gasar gudun famfalaki na kewaya filin wasa, wadda ya ci lambar gwal ta Olympic hudu da kuma shida ta duniya a gudun mita 5,000 da mita 10,000, ya koma gasar gudu a titi.

Kipchoge ya ce Farah dan Birtaniya, dan asalin Somalia gwanin dan tsere ne wanda ake mutuntawa, wanda kuma zai iya samun nasara ba tare da wani jinkiri ba, saboda haka ba zai yi sake da shi ba.

Farah mai shekara 34, kamar yadda aka tsara ya fice daga gasar ta gun-yada-kanin wani ta Landan a rabin nisan da za a kai a shekara ta 2013.

Sanna kuma a shekara ta 2014 ya kammala gasar a matsayi na takwas a cikin sa'a biyu, da minti takwas da dakika 21.