Kun san yadda za a fitar da jadawalin gasar Kofin Duniya?

Shirin fitar da jadawalin gasar kofin duniya ta 2018 Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Za a yi bikin fitar da jadawalin gasar kofin duniyar ta 2018 a zauren kade-kade na fadar gwamnatin Rasha ranar Juma'a 1 ga Disamba

Nan da kasa da sa'a 24 ne za a hada jadawalin gasar cin kofin duniya ta shekara mai kamawa a Rasha, inda jami'ai da manyan baki suka fara sauka a birnin Moscow domin halarta.

Najeriya tana tukunya ta karshe, wanda hakan ke nufin za a hada ta wasa da manyan kasashe a rukuninta, to amma kocinta dan Jamus Gernot Rohr ba shi da wata fargaba. Hasali ma ya ce zai so a hada tawagarsa ta Najeriya da kasarsa Jamus.

Daga bangaren Turai, akwai Rasha mai masaukin baki, da kasashen da suka zama na daya a rukunansu na sharar fage, wadanda suka kunshi Belgium da Ingila da Faransa da Jamus da Iceland da Poland da Serbia da Spaniya.

Akwai kuma kasashen Turan da suka samu tikitinsu na gasar bayan sun yi wasan raba gardama, wadanda su kuma sun hada da Crotia da Denmark da Sweden da kuma Switzerland.

Wakilan Afirka guda biyar a gasar ta kofin duniya kuwa su ne Najeriya da Senegal da Masar da Tunisia da kuma Moroccoa.

Daga Amurka ta Arewa da ta Tsakiya da kuma yankin Karebiyan, Costa Rica ce da Mexico da kuma Panama.

Ita kuwa Latin Amurka tana da Brazil da Argentina da Colombia da Peru da Uruguay, yayin da Asia take da Saudi Arabia da Iran da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Australia.

Za a yi zaman fitar da jadawalin na gasar ta cin kofin duniyar ne a zauren kade-kade na fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, gobe Juma'a 1 ga watan Disamba da karfe hudu na yamma agogon Najeriya.

Za a raba kungiyoyin kasashen ne bisa jerin sunayen gwanayen wasan na kwallon kafa da Fifa ta fitar na watan Oktoba na wannan shekara ta 2017.

Akwai tukwane guda hudu, a gaba daya, wadanda kowacce take dauke da tawagar kasashe takwas.

Za a sanya Rasha a tukunya ta farko tare da gwanayen kasashen da ke gaba guda bakwai, sai kuma guda takwas da ke bin baya a tukunya ta biyu.

Daga nan kuma sai gwanaye takwas na gaba a tukunya ta uku, yayin da su kuma takwas din karshe za a sa su a tukunya ta hudu.

Babu kasashen da suke daga nahiya daya in ban da na Turai (uefa) da za a hada su a rukuni daya. Kasashe mafi yawa da za a iya hada wa a kowane rukuni daga Turai, su ne biyu.

Tsohon dan wasan gaba na Ingila kuma mai gabatar da sharhin wasan kwallon kafa na BBC Gary Linker tare da 'yar jaridar harkokin wasanni ta Rasha Maria Komandnaya, su ne za su jagoranci taron.

Manyan bakin da za su halarci bikin za su hada da wakilai daga kowacce daga cikin kasashe takwas da suka taba cin kofin na duniya kamar haka;

Laurent Blanc (Faransa), da Gordon Banks (Ingila ), da Cafu (Brazil), da Fabio Cannavaro (Italiya), da Diego Forlan (Uruguay).

Sai kuma Diego Maradona (Argentina), da Carles Puyol (Spaniya) da kuma Miroslav Klose (Jamus).