An tuhumi kocin Chelsea Antonio Conte da rashin da'a

Kocin Chelsea Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Antonio Conte ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata, amma ya yi abin ne saboda yana wahala lokacin wasansu

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi kocin Chelsea Antonio Conte da laifin rashin da'a sakamakon korarsa da alkalin wasa ya yi lokacin karawarsu da Swansea City, saboda kin yarda da hukuncin lafirin.

A minti na 43 da wasan ne lafirin ya kore shi zuwa cikin 'yan kallo a fafatawar Premier da kungiyarsa ta yi nasara 1-0 a ranar Laraba.

Conte ya ci gaba da kallon wasan gaba daya ne na bayan hutun rabin lokaci a talabijin din dakin sanya tufafi na 'yan wasa, sakamakon korar saboda ya nuna rashin amincewa da hukuncin alkalin wasan na kin ba kungiyarsa bugun gefe lokacin ana canjaras a wasan.

Yana da wa'adin har zuwa ranar talata karfe shida na yamma agogon Najeriya, ya bayar da bahasi ga tuhumar in ji hukumar ta kwallon kafar ta Ingila.

Bayan wasan kocin dan kasar Italiya ya nuna nadama tare da bayar da hakuri a kan abin da ya yi.