Sam Allardyce ya kulla yarjejeniyar koci da Everton zuwa 2019

Sam Allardyce (a tsakiya) da mai kungiyar Everton Farhad Moshiri a Goodison Park Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dauki hoton Sam Allardyce (a tsakiya) tare da mai kungiyar Everton Farhad Moshiri a filinsu na Goodison Park ranar Laraba

Sabon kocin Everton Sam Allardyce ya ce yana matukar shauki da jin dadin dawowa aikin horarwa tare da kungiyar Everton.

Tsohon kocin na tawagar Ingila mai shekara 63 ya kulla yarjejeniya da kungiyar har zuwa watan Yuni na 2019, ta zama magajin Ronald Koeman, wanda aka kora a watan Oktoba, kungiyar tana matsayin ta 18 a teburin Premier.

Allardyce ba shi da aiki tun lokacin da ya bar Crystal palace a watan Mayu.

Yanzu dai Everton tana matsayi na 13 a gasar kuma za ta kara da Huddersfield a ranar Asabar.

Everton ta zama kungiyar Premier ta bakwai da Allardyce ya jagoranta, fiye da kowa ne koci, in banda Harry Redknapp wanda ya horar da kungiyoyi biyar.

Kocin bai taba faduwa da wata kungiya daga Premier ba, amma kuma sabanin haka ya kai Bolton da West Ham gasar da Championship.