Mourinho ya ce David de Gea gwani ne

David de Gea ya tunkude kwallo sau 14 a wasan. Hakkin mallakar hoto Julian Finney
Image caption David de Gea ya tunkude kwallo sau 14 a wasan.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce rawar da mai tsaron ragar kungiyarsa David de Gea ya taka ya nuna cewa shi fitaccen mai tsaron raga ne a duniya, bayan da United ta lallasa Arsenal da ci 3-1.

Dan kasar Spaniyan ya ture kwallo sau 14 a wasan, wanda hukumar tattara alkaluma ba ta taba samun haka ba a tarihi.

Mourinho ya kara da cewa, "kana bukatar mai tsaron raga ya zama cikin shiri a lokacin da kungiya take bukatarsa".

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce, rawar da De Gea ya taka ya cancanji a yaba mishi.

Sau 33 Arsenal tana kai hari ragar Manchester United, amma daya ne kwallo daya ce kawai ta shiga ragar golan.

Labarai masu alaka