Rashin 'yan sanda ya sa an dage wasan Tottenham da West Ham

'Yan kallon wasan Tottenham da Liverpool a watan Oktoba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tottenham ta jawo 'yan kallon da ba a taba samu ba a wasan Premier har 80,827 a karawarta da Liverpool a watan Oktoba

An dage wasan da Tottenham za ta yi da West Ham a ranar jajiberin sabuwar shekara mai kamawa ta 2018, a filin Wembley zuwa ranar 4 ga watan Janairu saboda matsalar tsaro.

Hukumar gasar Premier ta dauki wannan mataki ne bayan da hukumar da ke kula da filin ta rage yawan 'yan kallon da aka tsara za su shiga wasan tun farko zuwa dubu 43, kasa da rabin mutanen da filin wasan ke dauka ne.

Hukumomin sun dauki wannan mataki ne saboda za a tura jami'an tsaron da ke aiki a tashoshin jirgin kasa na karkashin kasa da ke kusa da filin wasan zuwa wasu sassan na birnin Landan.

Wasan wanda za a yi kwana biyu bayan Tottenham ta ziyarci Swansea, za a fara shi ne da karfe takwas na dare agogon Najeriya.