Man City: Cin wasa 20 ba kofi shirme ne - Kevin de Bruyne

Kevin de Bruyne na Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kevin de Bruyne ne ya ba wa David Silva kwallon da ya ci wa Manchester City ta doke West Ham

Dan wasan Manchester City Kevin de Bruyne ya ce bajintar cin wasa 20 a jere ba wani abu ba ne idan ba su dauki wani kofi ba a kakar bana.

De Bruyne ya ce idan ba su ci wani kofi ba a karshen kakar, akwai wanda zai yi wata magana ta cin wasa 20? Ba wanda zai damu da haka.

City ta yi nasara a wasa 14 daga cikin 15 na gasar Premier a kakar nan, inda ta yi canjaras a guda dayan, da kuma dukkanin wasanta biyar na rukuni na gasar cin kofin Turai.

Kungiyar tana gaban abokiyar hamayyarta Manchester United, da maki takwas a Premier, kuma za ta je ta kara da ita a Old Trafford ranar Lahadi.

Kafin karon-battar City za ta je Ukraine inda za ta kara da Shakhtar Donetsk a wasanta na karshe na rukuni na kofin zakarun Turai, wanda tuni ta tsallake zuwa mataki na gaba.

De Bruyne wanda ba zai yi wasan na Shakhtar ba saboda katin da aka ba shi, ya ce nasarar da suke yi a jere a jere tana da muhimmanci kuma tana ba su dama, amma suna da babban aiki a gabansu da Swansea da kuma Tottenham bayan wasansu da United.

Bal din da David Silva ya ci musu ana kusan tashi daga wasa a karawar da suka doke West Ham 2-1 ranar (jiya) Lahadi, da kuma idan suka doke United a karo na biyu a jere a karkashin jagorancin Pep Guardiola, za su zama daidai da Arsenal a bajintar da Gunners suka yi a Premier ta nasara 14 a jere a 202.