Kofin FA : Liverpool da Everton, Man Utd da Derby

Karawar hamayya ta Mersyeside; Liverpool da Everton Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Liverpool za ta kara da Everton a Premier ranar Lahadi, abin da ke nufin sabon kocin Everton Sam Allardyce zai yi wasan na hamayya biyu a sati shida na farko a aikinsa

Liverpool za ta kara da Everton, yayin da masu rike da kofi Arsenal za su fafata a gidan Nottingham Forest a wasannin zagaye na uku na gasar cin kofin FA.

Jagorar gasar Premier Manchester City za ta kara a gida da Burnley, yayin da Manchester United za ta karbi bakuncin Derby, sanna kuma Chelsea za ta je gidan Norwich.

Slough Town, wadda ita ce kungiya mafi kankanta a jadawalin da aka fitar za ta je gidan Doncaster idan har ta doke Rochdale ranar Litinin.

Wata karamar kungiyar Hereford za ta kara da Leicester, idan ta yi nasara a kan takwararta ta Fleetwood a wasan da za su sake.

Kungiyar AFC Fylde za ta je gidan kungiyar Premier ta Bournemouth idan har ta yi nasarar doke Wigan a wasan raba gardama. Woking, wadda ita ma karamar kungiya ce a gasar rukuni na biyar a Ingila, idan ta dace da nasara a kan Peterborough su ma a wasansu na biyu za su cancanci zuwa gidan Aston Villa.

A sauran wasannin AFC Wimbledon za ta je filin wasa na Wembley ta fafata da Tottenham, ita kuwa Middlesbrough za ta hadu da Sunderland yayin da Brighton & Hove Albion za ta karbi bakuncin Crystal Palace.

Za a yi wasannin ne a karshen makon 6-7 na watan Janairu na shekara mai kamawa ta 2018.